ALLAH ya yi wa Alkali Abdulkadir Orire da Alhaji Buhari Aminu Chiroma Rasuwa

Allah ya yi tsohon alkali Abdulkadir Orire rasuwa.

Tsohon alkalin ya rasu yana da shekaru 87 a duniya.

Shine alkalin farko na kotun daukaka karar Shari’ah a jihar Kwara Alkalin farko na kotun daukaka karar shari’ar Musulunci na jihar Kwara, Mai shari’a Abdulkadir Orire ya rasu.

Tsohon alkalin ya rasu a ranar Talata yayin da yake da shekaru 87 a duniya, gidan talabijin na TVC ya ruwaito.

Bayan sanar da rasuwar Alkali Abdulkadir Orire sai muka kara samun sakon rasuwar Barde Kerarriyan Zazzau, Alhaji Buhari Aminu Chiroma.

Allah ya yiwa Barde Kerarriyan Zazzau, Alhaji Buhari Aminu Chiroma, rasuwa, kamar yadda Masarautar Zazzau ta sanar da daren Talata.

Masarautar ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita inda tace: “Inalillahi wa inna illaihir rajiun, cikin alhini muke sanar da rasuwar Alhaji Buhari Aminu Chiroma, sabon Barde Kerarriyan Zazzau; Allahummaghfir lahu warhamhu wa sakkinhu fil jannah,.”

Rasuwar Alhaji Buhari Aminu Chiroma na zuwa ne kasa da mako uku da nada shi a sabon sarautar.

Marigayin na cikin sabbin mutanen da Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya baiwa sarauta makonnin baya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here