Dalilin Sallamar Hafsoshin Tsaro – Fadar Shugaban Kasa

 

Fadar shugaban kasa ta ce ba saboda gazawa bane aka sallami tsoffin hafsoshin tsaro ba.

An sallamesu ne saboda ana bukatar sabbin jini kuma da sabbin dabarun yaki.

Buhari ya jinjinawa tsoffin hafsoshin tsaron ta yadda suka bautawa kasar nan Fadar shugaban kasa a ranar Talaa ta ce abinda yasa aka sallami hafsoshin tsaro a yau ba saboda sun gaza bane.

Ta kara da cewa an yi hakan ne a wannan lokacin domin kara karfi a fannin yaki da ta’addanci tare da shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan.

Femi Adesina, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a fannin yada labarai, ya sanar da hakan a wata zantawa da yayi da Channels TV a kan siyasa kuma Punch ta kiyaye.

“Abinda yasa suka tafiya a yau ba yana nufin sun gaza bane. A gaskiya ba hakan bane. Kawai ana son sabbin jini ne da kuma sabbin dabarun yaki a kasar nan,” yace yayin da yake sanar da jinjinar da Buhari yayi wa tsoffin shugabannin tsaron.

“A takardar da shugaban kasar ya fitar a yau Talata, ya jinjinawa hafsoshin tsaron da suka tafi a kan gudumawar da suka bada wurin tsaron kasar nan.

Ya gamsu da ayyukansu ba kadan ba. “Wadannan da suke tafiya a yau sun kasance a kujerunsu na tsawon shekaru biyar da watanni biyar.

Lamarin na yin abinda ya dace ne a lokacin da ya dace,” Adesina ya kara da cewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here