Dalilin Hauhawar Farashin Kayayyaki – CBN
Gwamnan bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, ya danganta tsadar kayayyaki da bashin Naira tiriliyan 37.5 da aka baiwa gwamnatin tarayya.
A ranar 23 ga Mayu, 2023, majalisar dattijai ta amince da bashin ‘Ways and Means’ na Naira Tiriliyan 30 bisa bukatar Muhammadu Buhari.
Mista Cardoso ya ce dole ne ‘yan Najeriya su girbi abin da ke tare da karbar wannan bashin, yayin da ya ke bayyana matakan daidaita tattalin.
Read Also:
CBN ya fadi dalilin tsadar kayayyaki
Da yake magana a ranar Alhamis a wani taron Businessday, Mista Cardoso ya ce an kuma samu hauhawar farashin sakamakon kudaden da ke yawo sun yi yawa, inji rahoton The Cable.
Gwamnan bankin na CBN ya ce a yanzu Najeriya na girbar abin da ta shuka ne na karbo tulin bashi, wanda ya haifar da matsala ga tattalin arziki.
“Dukkanmu mun ga yadda bashin ‘Ways and Means’ ya haura zuwa N27trn kuma wani lamunin na N10.5trn. Dole bashin zai zo da matsala. A yanzu muna girbar sakamakon karbo bashin.”
– A cewar Cardoso.