Dan Wasan Najeriya, Oshimhen na Cikin Ƴan Takarar Gwarzon ƙwallon Afirka na 2023

 

Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen yana cikin ‘yan takara 30, da za a fiyar da gwarzon dan kwallon kafar Afirka na kakar 2022/23.

Mai taka leda a Italiya, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Napoli a gasar Serie A kakar da ta wuce mai 26 a raga.

Haka kuma shi ne na daya a yawan cin kwallaye a wasannin neman shiga gasar cin kofin Afirka mai 10 a raga har da hutun da ya ci a wasa daya.

Taurarin tawagar Morocco da ta taka rawar gani a gasar kofin duniya a Qatar a 2022 da suka zama na farko da su kai daf da karshe na cikin ‘yan takara.

Cikinsu har da mai tsaron raga, Yassine Bounou da Achraf Hakimi da Sofyan Amrabat da Hakim Ziyech da kuma Youssef en Nesyri.

Sadio Mane na Senegal da Mohamed Salah na Masar, wadanda suka lashe kyautar sau bibiyu, suma suna cikin ‘yan takara.

Walid Regragui, wanda ya ja ragamar Morocco, yana cikin ‘yan takarar koci 10 da ba kamarsa a 2023.

Mai takarar fitatcen dan wasan da ke taka leda a Afirka har Fiston Mayele na Jamhuriyar Dumukradiyyar Congo, wanda ya ci kwallo da yawa a CAF Champions League da CAF Confederation Cup a bara.

Kwararrun hukumar kwallon kafar Afirka ne suka fitar da gurbi bakwai da za a karrama wadanda suka taka rawar gani daga Afirka a 2022/23.

Daga baya za a bayyana ‘yan takara mata da suka taka rawar gani ‘yan Afirka a bara.

Za a yi bikin karrama wadanda za suyi nasara a birnin Marrakech ranar Litinin 11 ga watan Disamba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com