Murnar Zagayowar Shekarar Musulunci: Gwamnatin Jihar Osun ta Bayyana Ranar Labara a Matsayin Ranar Hutu
Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar shekarar Musulunci.
Adeleke, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 18 ga watan Yuli, ya ce an bayar da hutun ne domin shigowar shekarar 1445 bayan Hijirah.
A cewar sanarwar, gwamna Adeleke zai jagoranci wani fareti na musamman tare da al’ummar Musulmai a jihar.
Osogbo, jihar Osun – Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.
Kamar yadda rahoton Vanguard ya tabbatar, babban sakataren ma’aikatar cikin gida da ayyukan musamman ta jihar, Mudashiru Oyedeji, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Actors’ Strike Parallels ‘Black Mirror’ Plot About AI’s Impact on Hollywood Keep Watching.
Read Also:
Oyedeji ya bayyana cewa gwamna Adeleke ya bayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu ne saboda ba Musulmai damar yin murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Gwamna Adeleke zai jagoranci fareti na musamman a jihar
Ya ƙara da cewa domin murnar zagoyowar sabuwar shekarar, gwamna Adeleke zai jagoranci wani fareti na musamman tare da Musulmai a filin wasan ƙwallon ƙafa na Osogbo, a ranar Asabar 22 ga watan Yuli.
Wani bangare na sanawar na cewa:
“Domin murnar zagayowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1445 bayan Hijirah domin al’ummar Musulmin jihar Osun, gwamnan jihar Sanata Ademola Adeleke ya ayyana gobe, Laraba a matsayin ranar hutu a faɗin jihar.”
“A yayin da yake taya al’ummar Musulmai murna da fatan gudanar shagulgulan zagoyowar sabuwar shekarar lafiya, gwamnan zai jagoranci wani fareti na musamman ranar Asabar a filin wasan ƙwallon ƙafa na Osogbo a cikin jerin shirye-shiryen da aka shirya domin murnar zagayowar sabuwar shekara.”