Oyo: Majalisar ta Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 13 a Jahar
Majalisar dokokin jihar Oyo ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi goma sha uku.
An tattaro cewa an dakatar da su ne saboda kin bayar da hadin kai ga wani hukunci da majalisar ta zartar
Read Also:
Ciyamomin kananan hukumomin Akinyele ta gabas, Ido, Oluyole da Ibadan ta gabas na daga cikin wadanda abun ya shafa Majalisar dokokin jihar Oyo a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, ta sanar da dakatar da shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 13 a fadin jihar.
A cewar jaridar The Nation, an dakatar da su ne har sai baba ta gani saboda kin bin shawarar da majalisar jihar ta yanke.
Kananan hukumomi da abun ya shafa sune karamar hukumar Akinyele ta gabas, karamar hukumar Ido, karamar hukumar Oluyole, karamar hukumar Ibadan ta arewa maso gabas.
Sai karamar hukumar Lagelu ta yamma, karamar hukumar Soro da karamar hukumar Ogbomosho ta tsakiya, karamar hukumar Ogbomosho ta kudu.