Gwamnan Jahar Oyo ya Sauke Shugaban Jami’ar LAUTECH, Farfesa Micheal Ologunde
Gwamna Seyi Makinde na jahar Oyo ya sauke shugaban jami’ar LAUTECH, Farfesa Micheal Ologunde.
Olasunkanmi, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jahar ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a.
Gwamnan ya umurnin Farfesa Ologunde ya mika mulki ga jami’in da ke biye da shi a mukami domin cigaba da gudanar da harkokin jami’ar Gwamnan jahar Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya sauke shugaban Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola, Farfesa Micheal Ologunde kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin wata wasika da Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jahar, Olasunkanmi ya fitar a ranar Juma’a.
Read Also:
Wasikar ta ce, “Mai girma Injiniya Seyi Makinde, gwamnan jahar Oyo kuma mai ziyara a jami’ar Ladoke Akintola, ya umurci shugaban jami’ar Farfesa M.O. Ologunde ya sauka daga mukaminsa.
“Kazalika, an umurci shugaban jami’ar ya mika mulki ga jami’in da ke biye da shi a muƙami domin cigaba da gudanar da harkokin jami’ar.”
A baya, Makinde ya zargi shugaban jami’ar da ingiza ma’aikata su nemi a biya su albashin da suke bi bashi.
Makinde ya ce ya yi mamakin yadda ma’aikatan jami’ar suka fara magana kan albashin bayan an warware matsalolin da suka taso a jami’ar.
Gwamnatin na jahar Osun ta karɓe ragamar gudanarwa na jami’ar da a baya mallakar gwamnatocin Oyo da Osun ne.