Pakistan za ta Maida Hankali Ranar Juma’a a Kan Huɗubar Sunnonin Annabi Muhammad(S.A.W)
Mai bai wa Firai Ministan Pakistan shawara kan harkokin addini, Hafiz Tahir Mehmood Ashrafi ya ce a watannin Rabiul Awwal da Rabiul Saani, huɗuba a masallatan Juma’a za su mayar da hankali ne kan sunnonin Annabi Muhammad.
A lokacin wani taron manema labarai, ya ce an ɗamince da matakin ne a Majalisar Shura ta Pakistan da ke Punjab.
Read Also:
Ya ce za a riƙa gabatar da huɗuba kan batutuwa daban-daban kamar ilimin mata da haƙƙoƙinsuda hijabi da kawar da ta’adanci da amfanin ilimi da saurans
Ya ce yana da matuƙar muhimmanci a ilimantar da mutane kan yadda zamantakewa ta ke a Madina da kuma yadda shugabancin manyan Khalifan musulunci ya ke. Ya ce ana buƙatar haɗin kai don ganin an mayar da Pakistan kamar birnin Madina.
Ya kuma ce zai buƙaci ministan ilimin Punjab ya shirya muhawar da gasanni kan batutuwan addini a duka makarantun a faɗin ƙasar.