Patience Jonathan ce ta Taimakawa Wike ya Zama Gwamnan Ribas – Dino Melaye
Dino Melaye, dan takarar gwamnan PDP a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa ya sake caccakar Gwamna Nyesom Wike.
Melaye ya yi zargin cewa tsohuwar matar shugaban kasa Patience Jonathan ce ta dauki nauyin Nyesom Wike na jihar Ribas.
A cewar tsohon dan majalisar, Wike ya ki la’akari da mutanen da suka taimake shi har ya kai sama yayin da yake alfahari game da wadanda shi ya taimaka.
Rikicin da ke tsakanin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da Dino Melaye, dan takarar PDP a zaben gwamnan Kogi, ya dauki sabon salo.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa, Melaye, a wata hira da Arise TV, ya yi zargin cewa Patience Jonathan, matar tsohon shugaban kasa ce ta dauki nauyin Wike ya zama gwamnan jihar Ribas.
Read Also:
Tsohon sanatan ya kara da cewar tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da Peter Odili, sun ba da gagarumin gudunmawa a siyasar Wike, Premium Times ta rahoto.
Dan takarar gwamnan na Kogi ya zargi gwamnan Ribas da rashin godiya ga mutanen da suka taimaka masa har ya kai sama yayin da shi yake tunkaho game da mutanen da ya taimaka. Melaye ya yi ikirarin cewa tsohon gwamna Odili ya nada Wike ya zama shugaban karamar hukumarsa. Ya kara da cewar Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya nada gwamnan ya zama shugaban ma’aikatansa sannan ya zabe shi don zama ministan Najeriya.
Ya bayyana cewa tsohuwar matar shugaban kasar, Patience Jonathan, ta yi amfani da kudinta da hanyoyinta wajen tabbatar da ganin cewa Wike ya zama gwamnan jihar Ribas. Tsohon dan majalisar tarayyar ya bayyana cewa da ba don kokarin tsohuwar matar shugaban kasar ba, da Wike bai zama gwamnan jihar Ribas ba.
Wani bangare na jawabinsa na cewe:
“Misis Goodluck Jonathan ta kashe kudinta, hanyoyin da take da shi da komai don zamar da shi Gwamnan jihar Ribas.”