Paulinee Tallen: Ministar ta Kamu da Cutar Korona
Ministar al’amuran mata ta Najeriya Paulinee Tallen ta kamu da cutar korona.
Read Also:
Ministar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta aikawa manema labarai mai dauke da sa hannunta.inda tace cutar bata ci karfinta tukuna.
Adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona a Najeriya dai na ci gaba da karuwa a dai dai wannan lokaci.
A makon da ya gabata ne hukumomi suka sake rufe makarantu da wuraren shakatawa domin dakike yaduwar cutar.