PCACC ta na Shirin Karya Farashin Kayan Abinci a Fadin Kano

 

Hukumar yaki da rashawa da korafin jama’a ta jahar Kano, PCACC, tana shirin karya farashin kayan abinci a jahar.

Shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin tattaunawa da manema labarai.

A cewar sa, hukumar ta damu da yadda farashin kayan abinci a wurin ‘yan kasuwa suka tashi talakawa suna wahala.

Kano – Hukumar karbar korafin jama’a da yaki da rashawa ta jahar Kano, PCACC, ta bayyana shirin ta na karya farashin kayan abinci a fadin jahar.

Daily Trust ta rawaito cewa, shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis.
A cewarsa:

“Hukumar ta damu da yadda kayan abinci suka tashi a hannun ‘yan kasuwa wanda hakan ya na wahalar da talakawan jahar.”

Balarabe ya ce hukumar ba za ta tankwashe kafa tana kallon mugayen ‘yan kasuwa suna dora wa jama’a wahala ba, duk da tsananin rayuwar da kasar nan take ciki, Daily Trust ta wallafa hakan.

“Yanzu muna aiki a kan korafin jama’a ne da kuma yaki da rashawa. Muna aikin tare da majalisar jahar Kano don ganin sun sanya doka kuma mun tursasa ‘yan kasuwa sun karya farashin kayan abinci.

“Cikin dokokin akwai ci gaba da bincike a kan karin farashin kayan abinci da ‘yan kasuwa su ke yi a fadin jahar.

“Ganin halin tsananin rayuwar da jama’a suke ciki, sai mu ka ga ya kamata a ce mun sa ‘yan kasuwa sun daidaita farashin kayan abinci,” a cewar sa.

A cewarsa, dole doka ta tankwasa duk wanda ya yi kokarin bijirewa.

“Dole doka ta zama madubin al’umma. Ba za mu zura ido muna ganin mutane suna yin yadda suka ga dama ba,” a cewar sa.

Balarabe ya bayyana shirin su na ganin sun takwasa tarbiyyar yara ta hanyar samar da salon koya wa yara sana’o’i a makarantu don su girma da neman na kansu a zuciyoyin su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here