Osinbajo 2023: ‘Yan Kungiyar PCG Sun Kaiwa Gwamna Masari da Sarkin Daura Ziyara
Wasu ‘yan kungiyar PCG suna saida takarar Yemi Osinbajo a zaben 2023.
Progressive Consolidation Group tace Osinbajo ya fi dace wa ya karbi mulki.
‘Yan kungiyar sun ziyarci Katsina, sun gana da Gwamna da Sarkin Daura.
Katsina – Wasu daga cikin manyan jam’iyyar APC sun bayyana cewa babu abin da zai hana su goyon-bayan Farfesa Yemi Osinbajo a zabe mai zuwa.
‘Yan kungiyar Progressive Consolidation Group sun kai ziyara zuwa garin Katsina, inda suka gana da duka ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na kananan hukumomi 34.
Jaridar The Guardian ta ce ‘ya ‘yan kungiyar PCG sun gana da gwamna Aminu Bello Masari da mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.
Jagoran kungiyar PCG, Alhaji Aliyu Rabiu Kurfi, ya shaida wa manema labarai cewa sun yi nasara a wannan ziyara da suka kai zuwa jahar ta Katsina.
Read Also:
“Duk ranar Duniya, muna kara ganin abin da ke nuna nasarar da muke samu wajen wayar da kai da jan hankalin da muke yi na ganin Farfesa, Yemi Osinbajo ya gaji Muhammadu Buhari, ya cigaba a kan manufofin jam’iyyarmu ta APC.”
Shugabannin kungiyar PCG sun samu tarba
“Muna matukar godiya ga karramawa da tarbar da mutane da gwamnatin Katsina suka yi mana a lokacin da muka ziyarci gidan gwamnatin Katsina.”
“Haka zalika ziyarar da muka kai wa Mai girma, Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk a ranar Asabar.”
“Gwamna Masari da kansa ya tarbe mu, ya kuma bamu shawara mu yi amfani da karfin ‘ya ‘yan jam’iyyarmu wajen karfafa APC a fadin kasar nan.”
Aliyu Rabiu Kurfi ya shaida wa ‘yan jaridar cewa Sarkin Daura ya ji kiran da suke yi na ganin mataimakin shugaban kasa ya karbi mulki a zaben 2023.
Sakataren PCG, Dr. Eli Dibia ya bayyana cewa suna saida takarar Yemi Osinbajo ne domin a daura kan nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu.
A baya an ji kungiyar tana goyon bayan Yemi Osinbajo. PCG ta rubuta takardu tana cewa Farfesa Osinbajo ya kamata ya yi takarar kujerar shugaban kasa a APC.
Tawagar PCG sun hada da; Aliyu Rabiu Kurfi, Alhaji Ahmed Mohammed, Eli Eberechukwu Dibia, Olufemi Lawson, da kuma Jeffrey Omo Ozomegwa.
Sai kuma Ogechukwu Rose Micheal, Musa Gidado, Rabiu Daudu, Abubakar Mohammed Kent da Hon. Usman Yusuf.