Jam’iyyar PDP ta Bukaci Gwamna Hope Uzodinma da Yayi Murabus Daga Kujerarsa

 

Jam’iyyar hamayya ta PDP reshen jahar Imo tayi kira ga gwamnan jahar yayi murabus daga kujerarsa.

PDP tace gwamnan bashi da karsashi ko ƙwarin guiwar da zai fuskanci matsalar tsaron da take kara yawaita a jahar.

Jam’iyyar ta kuma sake yin kira da a gudanar da bincike mai zurfi a kan kisan da akai wa Ahmed Gulak, tsohon hadimin shugaba Jonathan.

Babbar jam’iyyar hamayya PDP, reshen jahar Imo ta kira yi gwamnan jahar, Hope Uzodinma, yayi murabus daga kan kujerarsa saboda ƙaruwar matsalar tsaro a jahar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a Owerri, babban birnin jahar, shugaban PDP na jahar Imo, Charles Ugwu, yace ga dukkan alamu gwamnan bashi da ta cewa a kan kashe-kashen dake faruwa a jahar.

PDP tayi kira da a gudanar da bincike mai zurfi kan kisan tsohon hadimin shugaban ƙasa, Ahmed Gulak, da akayi a jahar ranar Lahadi da safe.

Agwu yace gwamnatin jam’iyyar APC bata da karsashin da zata tabbatar da tsaron lafiyar al’umma da kare dukiyoyinsu.

Yace: “Gwamna Hope Uzodinma, a matsayinsa da abunda ya rataya a wuyansa amma ya gaza kare al’umma da dukiyoyinsu a jahar Imo.”

“Wannan abu ne a bayyane, gwamnatin APC ta gaza tabbatar da kare rayukan mutanen ta da dukiyoyin su duba da irin abubuwan dake faruwa a jahar.”

Shugaban PDP ɗin yace an jawo hankalin jam’iyyar su cewa ana kama wa tare da kashe matasan jahar da basu ji ba basu gani ba. Ugwu ya ƙara da cewa PDP ta damu matuƙa da irin cin mutuncin da akewa matasan jahar da kuma ƙona ofishin INEC da Caji Ofis.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here