Rashin Tsaro: PDP ta Caccaki Masari da Shugaba Buhari
Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Gwamna Aminu Masari da ya fito fili ya sanar da Buhari cewa ya gaza.
Sakataren yada labarai na babbar jam’iyyar hamayyar yace abun kunya ne yadda ‘yan bindiga suka kwace Katsina.
Kola yace shugaban kasa Buhari ya gaza domin dukkan alkawuransa na tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa sun kasa cika.
Katsina – Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci gwamna Aminu Masari na jahar Katsina da ya daina jaje kan hauhawar hare-haren ‘yan bindiga a jaharsa, TheCable ta wallafa.
A yayin karbar bakuncin Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa wanda ya kai ziyara jihar Katsina a ranar Alhamis, Masari ya ce goma daga cikin kananan hukumomin jahar na fuskantar harin ‘yan bindiga a kullum.
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya ce rashin tsaron da jahar Katsina ke fuskanta na hana shi bacci.
Read Also:
PDP ta caccaki Masari da shugaban kasa Buhari
A yayin martani ga zancensa, a ranar Lahadi, Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, yace ya dace Masari ya fito fili ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC cewa gwamnatin tarayya ta gaza.
Masari baya yi wa jama’arsa da suka fada tuggun ‘yan bindiga adalci.
Ganin yadda cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza kuma ya kasa tsare kasar nan. Ya saka siyasa a ransa ta yadda ya kasa sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari gazawarsa.
Tabbas abun takaici ne da gazawa irin ta shugaban kasa Muhammadu Buhari da za a ce ‘yan bindiga sun kwace kasarsa.
Sun kwace kananan hukumomi ta yadda suke kashe-kashe, fyade da halaka jama’a.
Shugaban kasa ya sha alwashin yakar ta’addanci amma yayi biris da kiran mutane yana cigaba da morewa a Aso Rock, Abuja. Abu ne sananne cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza.
Alkawurransa na tsaro, tattalin arziki da yaki da rashawa a bayyane suke ba zasu cika ba.