Abinda PDP Zatai ta ci Zaben 2023 – Raymond Dokpesi
Babban jigon PDP ya bayyanawa jam’iyyarsa abinda zatayi idan tana son nasara a 2023.
Dokpesi wanda ya nemi kujerar shugaban jam’iyyar a baya, yace gwanda su daina yaudarar kansu.
Yace PDP ta daina kokarin kwafan jam’iyyar APC.
Abuja – Babban jigon Peoples Democratic Party (PDP), kuma mammalakin gidan talabijin AIT, Raymond Dokpesi, yace PDP za ta iya cin zaben 2023 ne kawai idan ta fito da dan takara daga Arewa.
A hirar da yayi da jaridar Daily Independent, Dokpesi yace mambobin PDP dake cewa a baiwa dan kudu tikitin kujerar shugaban kasa na yi kawai don kwaikwayon APC ne.
Ya ce babu yadda za’ayi jam’iyyarsa ta PDP ta ci zaben shugaban kasa a 2023 idan ta gabatar da dan takara daga kudancin Najeriya.
Yace:
Read Also:
“Dukkanmu yan Najeriya ne kuma babu amfanin yaudarar kansu yanzu. A shekara 70 da kuma kwarewar da na samu wajen yakin neman zabe a kasar nan. ina tabbatar muku da cewa idan ba’a baiwa dan Arewa tikitin PDP ba, babu yadda za’a ci zabe.”
“Game da wadanda ke kudu suna kira ga a baiwa yan kudu tikiti, kawai suna kwaikwayo APC ne. A APC, Shugaba Muhammadu Buhari yayi shekaru takwas, saboda haka akwai bukatar ta mika shugabancin kasa kudu.”
Yan kudu sun fi na Arewa dadewa a kujerar shugaban kasa A cewarsa dan Arewa daya kacal, Umaru Yar’adua, ya yi mulki karkashin shekarar PDP.
Amma na kudu sun yi shekaru 14.
“Amma PDP, mu duba. Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo daga kudu maso yamma yayi shekara takwas; Goodluck Jonathan daga Kudu yayi shekara shida.Ka ga shekaru 14 kenan.”
“Amma Umaru Yar’adua daga Arewa yayi shekara 3, ka ga akwai banbancin shekaru 11 kenan.”