Rikicin Cikin Gida: Jam’iyyar PDP ta ‘Dage Taronta na NEC

 

Jam’iyyar PDP na kara dagulewa, ta dage wasu taruka guda biyu da za ta yi a makon nan masu muhimmanci.

Ana ta kai ruwa rana tsakanin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP da kuma gwamnan Ribas Wike.

Atiku ya zabi gwamnan jihar Delta Okowa a matsayin abokin takara, lamarin da ya kunno wutar rikici a inuwar lemar PDP.

Najeriya – Jam’iyyar PDP ta dage taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da ‘yan majalisar wakilai na kasa, biyo bayan dambarwar da ta dade tsakanin dan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ke kara dagulewa.

A tun da farko dai an shirya gudanar da tarukan gabobi biyu masu muhimmancin ne a gobe Laraba da kuma Alhamis, rahoton The Guardian.

Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya fitar, ta ce an dage zaman ne saboda wasu abubuwan da suka bullo da ba a yi tsammani ba.

Ya ce nan gaba kadan za a sanar da sabbin ranakun taron.

Duk da cewa sakataren bai bayyana dalilin da ya sa aka dage zaman, majiyoyin jam’iyyar sun ce sun yanke hakan ne sakamakon matsaya mai tsauri da gwamnan jihar Ribas ya dauka a yunkurin sulhunsu da Atiku.

Daga cikin wasu bukatu da yawa, sansanin na Wike ya yi kira ga shugaban PDP na kasa Dr. Iyorchia Ayu da ya sauka daga mukaminsa ya bar daya daga cikin mataimakansa daga Kudu ya karbi mukamin.

Sun nemi wannar kujerar ne ganin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da shugaban kwamitin amintattu (BoT) da shugaban kasa jam’iyyar duk ‘yan Arewa ne.

Wata majiya ta ce goron gayyatar da Wike ya yi wa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu zuwa kaddamar da ayyuka a jihar Ribas ta ruguza wasu fuka-fukai daga manyan jam’iyyar PDP.

A cewar majiyar, shawarar da Wike ya yanke na gayyatar gwamnan na Legas, wanda dan jam’iyyar APC ne, zuwa kaddamar da ayyuka a jihar da ke karkashin jam’iyyar PDP, ya faru ne saboda nuna rashin amincewa da shugabancin jam’iyyar.

Yadda Wike yake shigewa jiga-jigan APC, makusanta Tinubu

A ranar 8 ga watan Yuli ne Wike ya karbi bakuncin gwamnonin APC uku – Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Sanwo-Olu – kwanaki kadan bayan Atiku ya bayyana gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.

An ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ba su ji dadin yadda gwamnan na Ribas yake shigewa jiga-jigan jam’iyyar APC ba, musamman makusantan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Rahotanni sun ce Wike ya samu goyon bayan wasu manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da kuma kungiyoyi masu karfi domin ya samu kujerar mataimakin Atiku, inji The Nation.

Sai dai Atiku a ranar 16 ga watan Yuni, ya bayyana Okowa a matsayin mataimakinsa, sabanin shawarar da kwamitin tantancewa ya bayar, wanda ya ce Wike ne zai zama mataimakinsa.

Atiku ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP a ranar 29 ga watan Mayu da kuri’u 371 yayin da Wike ya zo na biyu da kuri’u 237.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here