Dr Mu’azu Babangida Aliyu: Jam’iyyar PDP ta Dakatar da Tsohon Gwamnan Jahar Niger

 

Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen jahar Niger ta dakatar da tsohon gwamna Dr Mu’azu Babangida Aliyu.

Jam’iyyar ta ce sanar da dakarwar ne a ranar Litinin a Minna bayan yin taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

Laifukan da ake zargin Babangida Aliyu da aikatawa na cin amanar jam’iyya sun hada da bawa jam’iyyar APC N450m a 2015 don kayar da PDP, raba kan yan jam’iyya dss.

Jam’iyyar PDP reshen jahar Niger ta dakatar da tsohon gwamnan jahar Niger, Dr Mu’azu Babangida Aliyu kan zarginsa da cin amanar jam’iyyar da hakan ya haifar da rabuwan kai a jam’iyyar tun 2014.

Hakan na cikin sanarwar bayan taro da jam’iyyar ta fitar a karshen taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da ta gudanar a garin Minna a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Sakon bayan taron da mutum 22 suka rattaba hannu a kai ya ce an dauki matakin kan tsohon gwamnan ne bayan shigar da korafi shida kansa wadda jam’iyyar a karamar hukumar Chanchanga ta lura abubuwan damuwa ne da ka iya hana jam’iyyar cigaba.

Kazalika, sakon bayan taron ya kuma bayyana cewa tsohon gwamnan ya yi aiki don ganin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da dan takarar gwamna a jahar Alhaji Umar Nasko sun fadi zabe ta hanyar taimakawa jam’iyyar adawa ta APC a 2015 da kudi Naira miliyan 450 don ganin jam’iyyarsa ta sha kaye.

Sakon bayan taron da aka raba wa manema labarai a jahar ta kuma ce zargin da ake masa sun hada da ‘raba kan yan jam’iyya duk da tarurukan sulhu da aka yi’.

Har wa yau, laifukan da ake zarginsa da shi sun hada da rashin hallartar taron jam’iyya da wasu ayyuka wanda hakan ya janyo rabuwar kai da rashin samun nasarar cimma manufofin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce, “wannan da wasu zargin da dama suka sa aka dakatar da Dr Mu’azu Babanigida Aliyu daga jam’iyyar Peoples Democratic Party a karamar hukumar Chanchaga ”. Shugabannin jam’iyyar takwas cikin gundumomi 11 ne suka samu hallarton taron.

An yi kokarin ji ta bakin tsohon gwamnan amma bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakonnin kar ta kwana ba a lokacin hada wannan rahoton.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here