Dan Takarar PDP ya Nuna Damuwa Kan Barazanar Tsaro a Zaɓen Jihar Edo

 

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Edo, Asue Ighodalo ya nuna damuwarsa kan barazanar tsaro a yayin da ake tsaka da kaɗa ƙuri’a a zaɓen.

Yayin da yake magana da manema labarai, Mista Ighodalo ya zargi ‘yansanda da kama ‘yan jam’iyyarsa a wata rumfar zaɓe.

“Arumfar zaɓe ta Uromi 3, wasu mutane ɗauke da makamai sun kama ɗaya daga cikin magoya bayanmu, a ƙa’ida babu wanda zai riƙe makamai a rumfar zaɓe, hakan ya sa ba wa doka, amma duk da haka sai ka ga mutane na abubuwan da ba su kamata ba, suna zaluntar jama’a tare da yunƙurin razanar da mutane,” kamar yadda ya bayyana wa manema kabarai.

Ya ƙara da cewa wannan al’amari na ɗaure masa kai, kasancewar magoya bayan jam’iyyar ne kawai ake kamawa.

”Ta yaya za a ce magoya bayan PDP ne kawai za a riƙa kamawa?, bayan ga ‘yan jam’iyyar APC nan na aikata abubuwan da ba su kamata ba, amma babu wanda ya kama su”.

Mista Ighodalo na PDP na samun gwamnan jihar Godwin Obaseki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here