Yadda Jam’iyyar PDP ta Samu Goyan Bayan Manoma Daga Jihohin Arewa 7
Kungiyoyin manoma na bangaren Arewa maso yammacin kasar nan sun yi zama da Dr. Baraka Sani.
Tsohuwar kwamishinar nomar ta Kano ta na cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar.
Dr. Sani ta saurari matsalolin da ke addabar masu noma, ta gabatar da masu manufofin PDP.
Kano – Wasu manoma daga jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun yarda za su goyi bayan takarar Atiku Abubakar na zama shugaban kasa.
Rahoton Premium Times na ranar Litinin ya bayyana cewa manoman sun yi magana a wajen wani taro da kwamitin yakin takarar PDP ya yi da su.
Wadannan manoma sun nuna cewa su na sa rai idan Atiku Abubakar ya karbi jagorancin kasar nan, zai yi maganin kalubalen da ke damunsu.
Masu harkar noma daga jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna, da Kebbi sun samu halartar wannan zama da aka yi kwanan nan.
Matsalolin da noma yake Fuskanta
Read Also:
Daga cikin matsalolin da ake addabar manoma a yankin Arewa akwai rashin tsaro, rikicin makiyaya da su manoman, da rashin gaskiyar ‘yan siyasa.
Alhaji Lawan ya ce baya ga matsalar tsaro, ‘yan siyasa su na yin uwa da makarbiya wajen rabon kayan noma, wanda yin hakan yana kawo nakasu.
Manomin ya ce a kudancin Sokoto, rashin tsaro ya jawo ba za su iya zuwa gonakinsu ba, ya kuma ce akwai bukatar saida taki tun wuri kuma da araha.
Nafi’u Muhammad wanda manomi ne daga Kebbi ya ce an san Zuru da Yawuri da noman dawa, amma yanzu ‘yan bindiga duk sun hana su sakat.
Shi kuma Shafa’u Yunus wanda yake kiwon kaji ya ce abin da suke nema wajen Atiku Abubakar idan ya hau mulki shi ne saukin abincin dabbobi.
Tsohuwar kwamishinar aikin gona ta jihar Kano kuma hadimar Goodluck Jonathan, Baraka Sani ta wakilci ‘dan takaran PDP a zaman da aka yi a Kano.
Vanguard ta ce Baraka Sani ta gabatar da manufofin Atiku, sannan tayi kira ga makiyaya da manoman su ba PDP hadin-kai ta dawo kan mulki.