PDP za ta Gyara Kura-Kuran da Tayi a Baya Idan Aka Bata Damar Jagorantar Kasar a 2023 – Gwamna Fintiri

 

 

Gwamna Ahmadu Fintiri na jahar Adamawa ya shawarci jam’iyyar PDP kan abubuwan da ya kamata tayi domin kwace mulki a 2023.

Fintiri ya ce babbar jam’iyyar adawar kasar na bukatar mutane masu mutunci domin yin nasara a babban zabe mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne gabannin babban taron jam’iyyar da za a yi a ranar 30 ga watan Oktoba.

Abuja – Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce jam’iyyar People Democratic Party (PDP) na bukatar mutane masu mutunci domin kula da harkokinta.

A cewar Fintiri, ta hakan ne kadai babbar jam’iyyar adawar za ta iya lashe zaben shugaban kasa a 2023, jaridar The Cable ta rawaito.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, a wajen taron jam’iyyar gabannin babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Oktoba.

Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a Abuja, Fintiri ya ce PDP za ta gyara kura-kuran da tayi a baya idan aka bata damar jagorantar kasar a 2023.

Ya ce:

“Duk mun san abubuwan da ke faruwa kamar yadda babban sakataren labaranmu na kasa da kansa ya bayyana – yadda muke cikin matsala a matsayinmu na kasa.

“Muna gab da tsallaka kuma dole muyi abun da ya kamata, tun daga wannan babban taron don tabbatar da ganin cewa mun zabi kwararru da za su jagorance mu da kwarewarsu da mutuncinsu domin ‘yan Najeriya su fara yarda da mu.

“Ya zama dole mu gyara dukkan kura-kuran da muka yi a baya. Shugabanninmu sun yarda cewa mun yi kuskure kuma mun ba ‘yan Najeriya hakuri. .

“Kuma da wannan, ina ganin akwai bukatar mu hada mutane masu mutunci domin su kula da harkokin jam’iyyar da kuma bamu damar nasara a zaben 2023, musamman kujerar shugaban kasa.”

Gwamnan ya kuma ce sai an hada kai da fata domin kai jam’iyyar ga matakin nasara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here