Kaduna: Jam’iyyar PDP ta Lashe Zaben Karamar Hukuma a Mazabar Gwamna El-Rufa’i

 

Gwamna El-Rufa’i ya rasa akwatin zabensa ga jam’iyyar PDP a zaben kananan hukumomi.

Gwamnan ya kada kuri’arsa da safiyar Asabar a akwatin zaben.

A cewar El-Rufa’i, ba dole bane jam’iyyarsa ta lashe kowani zabe ba.

Kaduna – Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP ta lashe akwatin zabe kujerar shugaban karamar hukumar da kuma na kansila a mazabar gwamnan jahar, Nasir El-Rufa’i.

El-Rufa’i ya kada kuri’arsa da safe a akwatin mazabarsa dake Unguwar Sarki, karamar hukumar Kaduna ta Arewa, rahoton ChannelsTV.

Yayinda yake kada kuri’arsa, El-Rufa’i ya bayyana cewa bai zama dole jam’iyyarsa ta APC ta kashe zabe ba, kawai abinda yake bukata shine inganta zabe ta hanyar amfani da na’urar zamani.

A cewar gwamnan, kawo wannan na’urar ua nuna cewa gwamnatin APC a jahar Kaduna ba tada shirin magudin zabe.

Yayin sanar da sakamakon zaben, baturen zaben mazabar, Muhammad Sani, ya ce jam’iyyar APC ta samu kuri’u 62 a zaben shugaban karamar hukumar, yayinda PDP ta samu kuri’u 86.

A zaben Kansila kuwa, APC ta samu kuri’u 53 yayinda PDP ta samu kuri’u 100.

Yanzu haka, ana cigaba da tattara sakamakon zabe a matattarar zabe na karamar hukumar Kaduna ta kudu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here