Gwamnonin PDP zasu Dauki Mataki Kan Shugaban Jam’iyyar

 

Burin shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, na yin tazarce a kujerarsa ya samu babban nakasu.

Majiya mai tsuhe ta sanar da cewa gwamnonin jam’iyyar PDP sun juyawa Secondu baya tare da fara neman wanda zai maye gurbinsa.

Neman wa’adin mulki na biyu ga shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, ya gamu da gagarumin tasgaro.

Hakan ya biyo bayan alamu da gwamnoni tsagin jam’iyyar ta hamayya ke nunawa akan cewa wataƙila ko za su sauya shi dab da ƙaratowar zaɓen 2023.

An gano cewar gwamnonin suna son Secondus, ɗan asalin jihar Rivers, ya sauka daga kujerar bayan ficewar gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi zuwa APC.

Akwai raɗe-raɗin da ke tasowa cewa akwai yiwuwar wasu da yawa su sake bin sahun Umahi sakamakon batutuwan da ke da dangantaka da irin zargin nuna kabilanci da bangaranci da Secondus ke yi a shugabancinsa.

Acewar Wata majiya mai tushe, gwamnoni sun tsaida shawara a cikin makon jiya bayan bayanai sun nuna cewa Sanatoci, ƴan majalisa da sauran fitattun jagororin jama’a sun dakatar da sauya sheƙar da suke niyyar yi.

Majiyar ta bayyana cewa masu son barin jam’iyyar PDP sun dakata ne har sai sun ga sabon shugabanci kafin ɗaukar matakin sauya sheƙar ta su.

Umahi, wanda ya bar PDP zuwa APC, ya ce ya bar jam’iyyar ne sanadiyyar rashin adalcin da jam’iyyar PDP ke yiwa yankin Kudu maso gabas.

“Bai dace ba ace tun daga shekarar 1999 har ƙaratowar 2023 ace ba’a taɓa baiwa Kudu maso gabas damar takarar shugabancin ƙasa ba. Wannan ba wai don kaina ba ne ko muradina,” a cewar Gwamnan jihar Ebonyi Umahi.

Ficewar gwamnan daga jam’iyyar da kuma raɗe-raɗen sauya sheƙar wasu da dama ya tayar da ƙura a jam’iyyar PDP.

Sannan kuma ana raɗe-raɗen mambobin jam’iyyar sun fusata ne sakamakon ɓangaranci a cikin jam’iyyar.

Sannan wasu gwamnoni sun nuna cewar kawar Secondus ne kawai zai kawo gyara da daidaito a al’amurran jam’iyya don yaƙar jam’iyyar hamayya ta APC.

Jaridar The Nation tattaro cewar a cikin satin nan, gwamnonin PDP sun yanke shawarar fara nemo wanda zai maye gurbin Secondus yadda ya dace a matsayin shugaban jam’iyyar.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gwamnonin sun haɗu a Abuja inda wasu suka haɗe da su ta kafar sadarwar Zoom don tattaunawa kan makomar shugaban jam’iyyar da kuma kwamitin aiwatarwa na jam’iyyar(NWC).

Wata Majiya tace; “a yanayin da ake ciki, bai wuce saura wata ɗaya wa’adin mulkin Secondus ya ƙare ba, ya zama dole jiga-jigan jam’iyyar su tattauna akan yadda za’a yi da Secondus da ƴan korensa.

“Haƙiƙa Shugaban jam’iyya na da burin cigaba da zama a kujerarsa, amma mafi yawancin gwamnonin jam’iyyar mu basu yarda da tsare tsarensa da shirinsa ba.”

“Kamar yadda yake, a halin yanzu gwamnoni na neman waɗanda zasu maye gurbinsa akan kujerar shugabanci jam’iyyar.”

“Akwai dalilan da yasa suke son chanja shi daga shugabancin jam’iyyar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here