PDP ta Mutu Muddin ta Kai Takara Zuwa Arewa a 2023 – Ohanaeze
Ohanaeze Ndigbo ta yi wa gwamnonin jahohin Arewa raddi game da batun 2023.
Kungiyar ta ja-kunnen jam’iyyar PDP kan ba ‘Dan Arewa tikitin shugaban kasa.
Kakakin Ohanaeze Ndigbo yace PDP ta mutu muddin ta kai takara zuwa Arewa.
Abuja – Kungiyar Ohanaeze Ndigbo mai kare hakkin mutanen Ibo ta gargadi jam’iyyar PDP a kan ba ‘dan Arewa tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Jaridar The Nation tace Ohanaeze Ndigbo ta fito ta maida martani a kan kalaman da kungiyar gwamnonin Arewa suka yi bayan zaman da suka yi a Kaduna.
Ohanaeze Ndigbo ta fitar da jawabi, tana cewa jam’iyyar PDP za ta mutu idan aka ba Arewa takara.
Mai magana da yawun bakin kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Alex Ogbonnia, yace an yi yarjejeniya a 1998 cewa mulki zai rika zagaya wa tsakanin kudu da Arewa.
Kungiyar take cewa an cin ma wannan yarjejeniya ne a 1998 a dakin babban taron NUC da ke Abuja, inda shugabannin Arewa da na kudu suka yi magana.
Read Also:
A cewar kungiyar, Dr. Chuba Okadigbo ya yi jawabi a madadin mutanen kudu, yayin da Marigayi Alhaji Abubakar Rimi ya yi jawabi da yawun bakin ‘Yan Arewa.
Mulki ya amfani ‘Yan Arewa?
Alex Ogbonnia ya zargi ‘yan siyasan Arewa da kokarin cigaba da mulkin kasar a lokacin da ake fama da matsalar ta’addanci da satar mutane a jahohin yankin.
Ogbonnia yace Arewa bai samu wani cigaban kirki ba duk da shugabannin da suka fito daga yankin a tarihi.
Shugabannin da aka yi daga yankin su ne; Abubakar Tafawa Balewa, Yakubu Gowon, Murtala Mohammed, Shehu Shagari, Muhammadu Buhari, Ibrahim Babangida.
Haka zalika an yi Sani Abacha, Abdulsalam Abubakar, Musa Yaradua, da Muhammadu Buhari.
Idan ‘Yan Kudu sun yi, sai ‘Yan Arewa su yi
“An yarda cewa bayan Janar Abdulsalam Abubakar, shugabanci zai koma Kudu. Wannan ya sa manyan jam’iyyu suka tsaida ‘yan takararsu daga yamma.”
“Olusegun Obasanjo ya yarda da wannan yarjejeniya, ya mika mulki ga Arewa, ya ba Ummaru Musa Yar’Adua.”
“Shi ma Goodluck Jonathan, mutumin kudu ya yarda da wannan yarjejeniya, ya damka mulki ga ‘Dan Arewa, a hannun Muhammadu Buhari.”