Jam’iyyar PDP ta Bukaci Shugaba Buhari da ya Sauke Rotimi Amaechi da Hadiza Bala Usman
Jam’iyyar PDP ta na so a sallami Rotimi Amaechi da Hadiza Bala Usman.
PDP ta ce akwai zargin da ke kan wuyan Ministan sufuri da mai dakinsa.
Jam’iyyar adawar ta bukaci a binciki shugabar NPA, Bala Usman da kyau.
Jam’iyyar PDP ta bukaci ayi maza a tunbuke babban Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da shugabar NPA da aka dakatar, Hadiza Bala Usman.
Jaridar Daily Trust ta ce mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP ya fito ya yi magana kan zargin cewa an wawuri N165b daga ma’aikatar NPA.
Kola Ologbondiyan ya bukaci Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya wanke kansa da mai dakinsa, Edith Amaechi, daga hannu a badakalar kwangila a NDDC.
PDP ta na zargin akwai hannun Ministan da iyalinsa da cin N48bn a badakalar kwangilolin da aka bankado a ma’aikatar da ke kula da yankin Neja-Delta.
Read Also:
Ya ce “Kazantar rashin gaskiyar da ta ke fito wa daga NPA, NDDC da sauran hukumomin gwamnati a shekaru shidan nan, ya nuna MDA sun zama saniyar tatsa kuma na’urar ATM a wajen hadamammun shugabannin APC da gwamnatinsu.”
Mista Kola Ologbondiyan ya na zargin Rotimi Amaechi da yunkurin kare kansa a badakalar da ake tafkawa a NPA cikin shekaru shidan nan da su ka wuce.
Bayan haka, NPA ta kashe N15bn wajen yin ayyukan taikmakon jama’a ba tare da an bi doka ba, don haka ta bukaci a sauke Darekta Janar din da Ministan.
“Hakan na zuwa ne bayan ofishin mai binciken kudi na kasa ya gano akwai satar N3,667,750,470. $148,845,745.04, £4,891,449.50 da £252,682.14 N3,667,750,470. $148,845,745.04, 4,891,449.50 da £252,682.14 a NPA.”
“Don haka PDP ba ta goyon bayan rufa-rufan da ake neman yi, a kafa wani kwamitin bincike da Ministan sufuri ya bada shawara domin a binciki aikin NPA.”
“’Yan Najeriya suna nuna Mai dakin Ministan sufuri da ‘dan yatsa kan zargin cin N48bn a karkashin tsohon shugaban NDDC da aka tsige, Nelson Bambraifa.”