Jam’iyyar PDP ta Jahar Zamfara ta ci Alwashin Zarcewa a 2023

 

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ita za ta ci gaba da rike jahar Zamfara a 2023.

A ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu ne aka shirya kungiyoyin adawa da ke cikin APC sannan suka sha alwashin kwato jihar daga hannun PDP.

Sai dai kuma PDP ta bayyana cewa dinkewar kungiyoyin APC din ba zai hana jam’iyyar adawar sake shan kaye ba a 2023.

Bayan yin sasanci tsakanin bangarorin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar Zamfara, wasu jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun jadadda cewa babu abunda zai hana Gwamna Bello Matawalle zarcewa a 2023.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa PDP wacce ke mulki a jahar ta ce hukuncin bangarorin APC na hadewa ba zai shafi nasararta ba a zabe mai zuwa.

Legit.ng ta tattaro cewa gabar da ke tsakanin sansanin tsohon gwamna Abdulaziz Yari da tsohon sanata Kabiru Garba Marafakan zaben fidda gwani na gwamnan APC a jihar a 2019 ne ya ja masu shan kaye.

Gwamnan jahar Yobe kuma Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ne ya shirya Yari da Marafa a ranar Litinin, 1 ga watan Fabrairu.

Sai dai kuma wasu masu biyayya ga PDP wadanda suka yi martani kan ci gaban, sun ce sasancin ba zai shafi jam’iyyaarsu ba a zaben 2023.

Kakakin PDP a jihar, Alhaji Farouk Ahmad, ya ce:

“Shirinsu ba zai shafi kuri’un da PDP za ta samu ba a zabe mai zuwa.Magoya bayanmu na nan kuma har yanzu muna tare da su. Don haka babu abun tashin hankali.”

Mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Ma’aji Gusau, shima ya ce shirin ba zai shafi nasarar jam’iyyar a jahar ba.

Ya ce:

“Mutane ne za su zabi wanda suke so a karshe. Su za su yanke shawarar zabar A ko B kuma wannan ba zai janye hankalinmu daga abunda muke yi don sauya rayukan jama’a a jahar ba, kuma ma mutane ne ke da ikon yin chanji.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here