Jam’iyyar PDP na Gudanar da Zanga-Zanga a Ofishin INEC da ke Abuja
Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya na gudanar da wata zanga-zanga a shalkwatar hukumar zaɓen ƙasar INEC a Abuja babban birnin ƙasar.
Shugaban jam’iyyar na ƙasar Iyorchia Ayu, da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen da aka gudanar gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta na daga cikin mutanen da suke jagorantar zanga-zangar.
Read Also:
A wata sanarwar da Ibrahim Bashir ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar ya fitar a madadin daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, ya ce daga cikin mutanen da aka gayyata zuwa zanga-zangar sun haɗar da shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wato gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel, da daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar wanda shi ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
“Gwamnonin jihohin Bayelsa da Edo da Adamawa da Bauchi da Taraba da kuma Osun States, sauran su ne tsoffin shugabannin majalisar dattawan ƙasar Sanata David Mark da Sanata Abubakar Bukola Saraki, da kwamitin amintattun jam’iyyar da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai na jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na daga cikin mutanen da suka halarci zanga-zangar”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta kuma umarci jami’an da su sanya baƙin tufafi domin nuna ɓacin ransu a zanga-zangar da za su gudanar a Maitama da ke Abuja.