Gobara ta ƙone ƙauyuka 3 a Jihar Jigawa

 

Wata mummunar gobara da ta tashi a wasu ƙauyuka uku a cikin ƙaramar Kiyawa a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta janyo asarar dukiyoyi masu yawa.

Gobarar ta yi sanadin ƙonewar ɗaruruwan gidaje da amfanin gona da kuma dabbobi masu yawa.

Al’amarin ya auku ne ranar Lahadi da rana a ƙauyukan Malamawa da Karangiya da kuma Kwaleji.

Mutanen ƙauyukan sun kwana a bayan gari saboda gobarar ta ƙone musu gidajensu.

Rahotonni sun ce an kwashe lokaci mai tsawo kafin a iya kashe wutar sakamakon iskar da ke kaɗawa a kauyukan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here