PDP ta Zargi APC da Tafka Maguɗi a Zaɓen Edo
Jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Edo da aka yi a ranar Asabar, wanda Hukumar INEC ta sanar da ɗan takarar APC Sanata Monday Okpebholo a matsayin wanda ya yi nasara.
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda shi ne shugaban kwamitin yaƙin zaɓen PDP na Edo ne ya yi zargin, inda ya ce INEC ta karya dokokin zaɓe.
A zaɓen, Monday Okpebholo ya samu ƙuri’a 291,667, inda ya doke abokin karawarsa na PDP, Asue Ighodalo wanda ya zo na biyu da ƙuri’a 247,274.
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya fitar, ya ce Fintiri ya gabatar da sakamakon zaɓen da ke nuna ɗan takarar PDP ne ya lashe zaɓen.
“PDP tana nan kan bakanta na sakamakon zaɓen da aka tattara daga akwatunan kaɗa ƙuri’a, wanda kuma shugaban kwamitin PDP na zaɓen, Ahmadu Fintiri ya tattara, inda sakamakon ya nuna ɗan takarar PDP Dr. Asue Ighodalo ne ya lashe zaɓen,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Read Also:
PDP ta yi zargin cewa daga baya APC ta samu nasarar tafka maguɗi a zaɓen tare da sa hannun wasu gurɓatattun jami’an INEC.
Ita ma ƙungiyar gwamnonin PDP, ƙarƙashin shugabanta gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ta buƙaci INEC ta riƙa gudanar da aikinta da “ba sani ba sabo.” domin samun amincewar al’ummar ƙasar, sannan ta buƙaci hukumar zaɓen da ta bayyana asalin sakamakon abin da mutanen Edo suka zaɓa kamar yadda muka kalato daga jaridar Punch.
A gefe guda kuma, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi na’am da sakamakon zaɓen, sannan ya yaba da yadda aka kaɗa ƙuri’a cikin lumana.
Tinubu ya kuma yaba wa shugabannin APC na ƙasa da na jihar Edo da gwamnonin jam’iyyar bisa ƙoƙarin da suka yi.
Ya ce nasarar na nuna cewa mutanen Najeriya suna goyon bayan jam’iyyar APC da shirye-shiryenta na farfaɗo da tattalin arziki da jin daɗin ƴan Najeriya.
A ƙarshe ya yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan da ya kasance na kowa, sannan ya haɗa kai da abokan karawarsa domin ciyar da jihar Edo na gaba.
“Sannan ina yaba wa INEC da jami’an tsaronmu bisa ƙoƙarin da suka yi na tabbatar da an gudanar zaɓen nan cikin lumana. INEC ta ƙara nuna shirinta na gudanar da zaɓe sahihi a ƙasar nan,” in ji Shugaba Tinubu.