Bayan Kisan Matafiya 25: Gwamnatin Jahar Plateau ta Saka Dokar Hana Fita na Sa’o’i 12 a Jos
Gwamnatin jahar Filato ta yi Allah wadai da kash-kashen da aka yi wa wasu matafiya a jahar.
Gwamnati ta gaggauta sanya dokar hana fita domin shawo kan lamarin da kwantar da tarzoma.
A halin yanzu, an umarci kowa ya zauna a gida daga karfe 6 na yammaci zuwa 6 na safiya.
Jos, Filato – Biyo bayan kashe kashen da aka yi a Jos ranar Asabar, gwamnatin jahar Filato ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 12 a Jos a kullum daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Wannan na fitowa ne daga gwamnan jahar ta Filato, Dr Simon Bako Lalong a jiya Asabar 14 ga watan Agusta, 2021 jim kadan bayan tabbatar da kashe-kashen.
Wata sanarwa da gwamnan ya fitar, wacce Legit Hausa ta samo ta nuna gwamnati ta tabbatar da faruwar kashe-kashe a garin, hakazalika ta sanya dokar ta baci.
Wani yankin sanarwar na cewa:
Read Also:
“Domin kaucewa ci gaba da tabarbarewar lamarin da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, na ba da umarnin sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Bassa da Jos ta Kudu da zai fara daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe daga yau, 14 ga Agusta 2021.
“Dokar hana fita za ta ci gaba da kasancewa inda kwamitin tsaro na Jaha zai sake dubawa.
“Don haka ana umartar dukkan mazauna da su bi umarnin don ba jami’an tsaro damar kiyaye doka da oda a yankunan da abin ya shafa da kuma magance wadanda ke kokarin haifar da matsala ta hanyar amfani da yanayin don aikata laifi.
“Gwamnati za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da daukar karin matakan da suka dace don tabbatar da tsaron rayuka da kadarori.”
Gwamna ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu
Hakazalika, gwamnan jahar ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, tare da jajantawa wadanda suka ji raunuka.
A cewarsa:
“A yayin da nake ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, da wadanda suka jikkata a lamarin da bai yi dadi ba, ina kira da a kwantar da hankali tare da yin kira ga ‘yan jiharmu da su guji duk wani mataki ko maganganun da za su kara rura wutar lamarin.
“Wannan zunzurtun ta’addanci ne kuma bai kamata a ta’allaka shi da kabila ko na addini ba.
“Mu ci gaba da yin taka tsantsan da sanin ya kamata game da tsaro tare da yin duk mai yuwuwa don wanzar da zaman lafiya da tsaron jahar.