PTF ta Gano Adadin Mutanen da Suka Shigo Najeriya ba Tare da Sunyi Gwajin Korona ba

 

PTF za ta dauki mataki a kan masu shigowa ba tare da gwajin Coronavirus ba.

Gwamnatin Tarayya za ta rike fasfo da takardun bizan irin wadannan mutane.

Doka ta bukaci ayi wa wadanda su ka zo Najeriya gwaji kafin su shiga.

Jama’a Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta wallafa lambobin fasfon mutane 100 da za a dakatar da takardun barin kasarsu na tsawon watanni shida.

Hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi ya sanar da wannan mataki da aka dauka a shafin Twitter.

Gwamnati ta dauki wannan mataki ne a dalilin saba doka da mutanen su ka yi, su ka shigo Najeriya daga kasar waje ba tare da an yi masu gwaji ba.

A doka duk wanda ya shigo cikin Najeriya, zai killace kansa, a kwana na bakwai za ayi masa gwaji domin tabbatar da bai dauke da kwayar COVID-19.

Kwamitin PTF mai yaki da cutar COVID-19 ta ce ta tuntubi wadannan mutane 100 da su ka shigo Najeriya, kuma sun tabbatar mata ba su yi gwajin ba.

PTF da shugaban kasa ya kafa ta ce za a dakatar da fasfon duk wadanda aka samu da wannan laifi, sannan za a karbe takardun bizan baki daga waje.

“Hukuncin zai yi aiki a kan mutanen da aka samu su na gabatar da takardun sakamakon gwajin PCR na bogi domin su yi tafiya.” Inji kwamitin na PTF.

A cewar kwamitin, akwai wasu ‘yan Najeriya da ke yin wannan danyen aiki, domin su saye tikitin jirgi ko su gabatar da su a tashar filin jirgin sama.

An bukaci a rika tantance lafiyar wadanda su ka zo daga ketare ne domin tabbatar da cewa ba su cakudu cikin sauran jama’a da ke cike da koshin lafiya ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here