Shugaban Rasha, Putin da Kim Jong-Un Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Shigarwa Juna Faɗa
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaran aikinsa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un sun sanya hannu kan abin da Putin ya bayyana a matsayin “gagarumar” yarjejeniyar taimakon juna.
Read Also:
An sanya hannu kan yarjejeniyar ce a yau Laraba, a wani ɓangare na ziyarar da shugaba Putin ke yi a Koriya ta Arewa, karo na farko a cikin sama da shekara 20.
Babu ƙarin bayani kan abin da yarjejeniyar ta ƙunsa.
Lokacin ziyarar tasa, an yi wa Putin tarba ta ban-girma wadda ta haɗa da faretin sojoji da kuma miƙa furanni.
Mista Kim ya bayyana cewa yana goyon bayan samamen da Rasha ke yi a Ukraine ɗari bisa ɗari.
Vladimir Putin a nasa ɓangaren ya ce akwai buƙatar sake duba takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙaƙaba wa ƙasar ta Koriya ta Arewa.