Kotu ta Raba Auren Mutumin da ya Auri Jikarsa a Zamfara

 

Wata babban kotun shari’a a karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara ta warware aure tsakanin wani mutum da jikarsa.

Mutumin mai suna Musa Tsafe ya auri jikarsa mai suna Wasila ne tun shekaru 23 da suka gabata kuma har sun haifi yara guda takwas.

Hukumar Hisbah, wacce ta yi kararsa a kotun ta ce tun shekarar 2020 ake ta fama da shi ya saki matar amma abin ya ci tura duk da binciken da aka yi ya nuna jikarsa ce.

Zamfara – Wata babban kotun shari’a da ke Tsafe, a karamar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara a ranar Talata ta raba auren shekaru 23 tsakanin wani mutum Musa Tsafe da jikarsa, Wasila.

Yayin yanke hukuncin, alkalin kotun, Malam Bashir Mahe, ya raba auren bayan ya saurari bangarorin biyu wato masu kare da wadanda aka yi kara.

Mahe ya ce auren tsakanin Tsafe da Wasila bai hallarta ba a koyarwar addinin musulunci.

Alkalin ya ce aure tsakanin mata da mijin ya saba wa sura ta 3 aya ta 23, shafi da shafi na 79 da 77 na ihkamil Ihkami.

Ya yi bayanin cewa an yanke hukuncin ne bayan wanda aka yi kara ya gaza kare kansa daga zargin da aka shigar kansa.

Hukumar Hisbah ne ta shigar da kara inda ta nemi a raba auren na shekaru 23. Hisbah ta shaidawa kotu cewa auren tsakanin Tsafe da Wasila ya saba wa dokokin addinin musulunci da shari’a.

Hukumar ta ce hakan ya tilasta mata shigar da karar bayan Kwamitin Shura da masarautar Tsafe tun 2020 sun yi kokarin raba auren amma bai yiwu ba.

Binciken da kungiyoyin musulunci da dama suka yi ya nuna jikarsa ce, Hisbah

Lauyan hukumar Hisbah, Malam Sani Muhammad, ya shaida wa kotu cewa binciken da kungiyoyin musulunci da dama suka yi ya nuna cewa akwai alaka ta jini tsakanin ma’auratan da suka yi aure tun 1999 don haka auren bai hallasta ba.

Muhammad ya ce auren ya saba da koyarwar addinin musulunci kamar yadda ya zo a sura ta uku aya na 23 a cikin alkur’ani mai girma. Don haka, ya roki kotun ta raba auren.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa Tsafe ya haifi yara takwas tare da Wasila.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here