Sabon Gwamnan Katsina, Dr.Radda ya Fitar da Jerin Mukamai 11
Sabon Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda ya fitar da wadanda za su rike masa mukami.
Arch. Ahmed Musa Dangiwa ne zai rike kujerar Sakataren gwamnati a mulkin Dikko Umaru Radda.
An fitar da sunayen hadiman farko tun a ranar da Alkalin Alkalai Musa Danladi ya rantsar da Gwamna.
Katsina – Jim kadan bayan ya yi rantsuwa a matsayin sabon Gwamna a jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda ya sanar da wasu mukamai da ya nada.
A wani jawabi da sabon Gwamna ya sa hannu da kan shi wanda Isah Miqdad A. D Saude ya fitar a shafinsa, ana sabon sakatare da wasu manyan hadimai.
Arch. Ahmed Musa Dangiwa ya zama sakataren gwamnatin Katsina, Gwamna ya nada Mal. Maiwada Danmallam a kujerar Darekta Janar na yada labarai.
Masu rike da gidan gwamnati
Read Also:
Alh. Jabiru Tsauri ya zama shugaban ma’aikatan fadar Gwamna, Muhtar Aliyu Saulawa ya zama mataimakinsa. Ahmed Rabiu shi ne mai daukar hoto.
Sanarwar ta ce Ibrahim Kaula Mohammed ya zama babban sakataren yada labarai na Gwamna Dikko Umaru Radda wanda ya shiga ofis a ranar Litinin.
Malam Miqdad Isah ya zama babban mai taimakawa Gwamna a kafofin sadarwa na zamani, Abubakar Badaru Jikamshi zai kula da sauran gidajen labarai.
Ofishin Mataimakin Gwamna
Bishir Maikano ya zama babban hadimi a ofishin mai girma mataimakin Gwamnan Katsina.
Kamar yadda Isah Miqdad ya sanar, sauran mukaman da aka nada a wannan ofishi sun hada da Alh. Hassan Ibrahim Danhaire (harkoki na musamman).
A karshe Mai girma Gwamnan ya taya wadanda aka ba mukaman murna, ya kuma yi kira gare su, su yi aiki da shi wajen ganin an kawowa jihar cigaba.
Da ya ke magana a shafinsa, Isah Miqdad ya nuna farin cikinsa a kan yadda aka ba shi wannan matsayi, ya ce ba zai taba yin wasa da wannan dama ba.