Jiga-Jigan PDP da APC Sun Nuna Ra’ayinsu Akan a Bawa Matasa Ragamar Kula da Shugabancin Kasa

An ƙarfafa wa matasan Najeriya gwiwar cewa su shirya don jagorantar kasar bayan zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Wasu manyan jiga-jigan PDP da APC da suka yi taro a Abuja a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, ne suka yi wannan kiran ga matasa.

Daya daga cikin ‘yan siyasar, Sanata Eyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, ya lura cewa lokaci ya yi da matasa za su yi aikin gyara kasar.

Abuja – ‘Yan siyasar Najeriya daga yankin kudu maso gabas sun yi amanna kan cewa lokaci ya yi da za a bai wa matasa ragamar kula da shugabancin kasa.

Wadanda suka gabatar da wannan ra’ayi a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, yayin wani shiri na Jakadan Matasan Najeriya a kasashen waje (NDYA) wanda aka shirya a Abuja sun hada da Sanata Eyinnaya Abaribe, Rochas Okorocha, da Orji Kalu da sauransu, PM News ta ruwaito.

Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya lura cewa ya kamata matasa masu kishi da son gyara batutuwan da ke addabar kowa su dare kujerun shugabanci na gaba.

Sanatan na PDP ya kara da cewa a halin yanzu majalisar kasa na aiki a wani bangare na kundin tsarin mulkin Najeriya don ba matasa damar shiga cikin harkokin siyasa.

Ya ce:

“Majalisar kasa a halin yanzu tana yin bitar kundin tsarin mulki don duba dukkan sassan kundin tsarin mulkinmu da ke bukatar gyara don amfanin kowa.

“Muna kuma duba hanyoyin da za mu ba matasa dama don su shiga a dama da su a shugabancin Najeriya.”

Da yake bayyana ra’ayin Abaribe, Babban bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Kalu, (APC, Abia) ya lura cewa majalisar dokokin Najeriya tana da nasaba da matasa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here