Za mu Rage Hauhawar Farashin Kayayyaki da Kashi 21 a Cikin 100 – Shugaba Tinubu

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata domin rage hauhawar farashin kayayyaki da kashi 21 cikin 100 a shekarar mai zuwa.

Yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin ƙasar, shugaba Tinubu ya ce hakan zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Najeriya dai na fama da hauhawar farashin kayayyaki musamman bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kara da cewe, gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata don magance matsalolin da suka daɗe suna ci wa fannin ilimi tuwo a ƙwarya.

Yayin da yake jawabi a lokacin gabatar da kasafin kuɗin ƙasar, shugaba Tinubu ya ce ”za a yi hakan ne ta hanyar aiwatar da wani tsari mai ɗorewa na tallafin karatu, ciki har da tsarin bashin karatu na ɗalibai da aka tsara zai fara aiki nan da Janairu 2024.”

Makarantun Najeriya dai na fama da matsaloli masu tarin yawa, ciki har da yajin aikin malamai da ƙarin kuɗin makaranta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com