Rashin Adalci: Daga Fadar Gaskiya An Rage wa Wani Soja Matsayi

Hukumar Soji ta hukunta wani babban jami’inta kan saba dokar amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

An hukunta Janar Adeniyi tare da hadimin na musamman.

Sojan ya lashi takobin daukaka karan hukuncin da aka yanke masa.

Wata kotun Sojoji da zamanta a Abuja ta kama Manjo Janar, Olusegun Adeniyi, tsohon kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, da laifi.

Kotun ta rage masa matsayi da shekaru uku.

Adeniyi, wanda Manjo Janar ne ya bayyana a wani bidiyo a watan Maris inda yake kuka kan rashin makaman yaki da Boko Haram a Arewa maso gabas.

Daya daga cikin wadanda suke tare da shi suka saki bidiyon a yanar gizo.

Ba tare da bata lokaci ba aka cireshi daga matsayin kwamandan Operation Lafiya Dole kuma aka tura cibiyar dukiyoyin sojin Najeriya dake Abuja.

Daga baya aka mayar da hedkwatar Soji dake Abuja inda yake gurfana a kotun Sojoji.

Yayin yanke hukunci kansa ranar Litinin, kotun ta kama Adeniyi da laifin saba ka’idojin gidan Soja kuma ta bada umurnin rage masa matsayi da shekaru akalla uku, The Cable ta ruwaito.

Hadiminsa, Tokunbo Obanla, wanda aka gurfanar da su tare da Janar, shi ma an kama shi da laifi kuma an yanke masa hukuncin daurin makonni hudu a kurkuku da mugun wahala.

Lauyoyin Adeniyi sun ce zasu daukaka kara gaban wata kotun

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here