‘Yan Sintiri Sun yi Ram da Masu Garkuwa 10 a Dajin Kwara
‘Yan sintiri a jihar Kwara sun yi ram da wasu mutum goma wadanda ake zarginsu da addabar yankunan Obbo-Aiyegunle zuwa Ekiti.
Kamar yadda kwamandan hukumar sintiri, Alhaji Saka Ibrahim ya sanar, an kama su ne a daji yayin da jami’ai suka kai samame.
Ya sanar da cewa har yanzu mutanensu suna cikin daji kuma za su mika wadanda aka kama ga jami’an ‘yan sanda.
Kwara – Wasu mutum goma da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi yankin Obbo-Aiyegunle zuwa Ekiti a jihar Kwara sun shiga hannun hukuma.
Read Also:
An damke su ne bayan samamen da jami’ai suka kai wata maboyarsu da ke daji inda ake zargin suna adana wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Yankin a cikin kwanakin nan ya shahara ta yadda masu garkuwa da mutane ke sace mutane kuma a kan samu gawawwakinsu bayan an biya kudin fansa.
Kwamandan hukumar sintiri ta jihar Kwara, Alhaji Saka Ibrahim, ya tabbatar da aukuwar lamarin ta wata tattaunawar waya da Daily Trust.
Kamar yadda yace:
“An damke wasu mutum bakwai a ranar Talata yayin da aka cafke wasu uku a ranar Laraba. Amma har yanzu jami’anmu na duba dajin. Za mu mika su hannun ‘yan sanda idan sun fito daga dajin.”