Mutane 22 Sun Rasa Rayukansu Bayan Harin da Rasha ta Kai Birnin Sumy na UKraine

 

Mun sami karin bayani kan wani hari da Rasha ta kai da yayi sanadin mutuwar mutum 22 – cikinsu har da kananan yara uku – a birnin Sumy na kasar Ukraine.

Gwamnan yankin Sumy Dmytro Zhyvytskyi ya ce cikin dare Rasha ta harba bama-bamai ne ayankin da fararen hula ke zama wanda ke arewa maso gabashin birnin, inda ya ce kisan kiyashi ne Rashar ta yi.

Ya shaida wa BBC Ukrainian cewa: “Bama-bamai uku cikin dare daya… Abin babu kyawun gani.”

harin ya halaka mutum uku da ke zaune tare cikin gida daya. Ya kuma lalata gidaje uku baki dayansu, inda wasu gidaje 20 kuma aka lalata su sosai.

Kamar yadda muka fadi a baya, mutum 5,000 sun sami ficewa daga birnin na Sumy, bayan da Rasha ta amince ta dakatar da bude wuta kan birnin domin a bude wa fararen hula hanyoyin jin kai na barin birnin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here