Watan Ramadan: Ana Ci gaba da Fafatawa a Khartoum
Alamu sun nuna cewa tsagaita wuta a watan Ramadan a Sudan zai yi wahala bayan sojojin ƙasar sun sanar da cewa sun sake ƙwato shelkwatar gidan labarai na kasar da ke Omdurman.
Wani shafin intanet ya rawaito cewa babban hafsan sojoji Janar Abdel Fattah al Burhan yayi alkawarin fatattakar dakarun-RSF daga koina har sai “nasara ta samu”.
Yayi maganar ne yayin ziyarar sojoji a birnin wanda yake a tsallaken kogin maliya daga babban birnin Khartoum.
Dakarun na RSF sun ƙwace ginin gidan talabijin da rediyo na ƙasa bayan ɓarkewar faɗa a watan Afrilun shekarar da ta gabata sannan har yanzu ba su wallafa komai ba kan kwace shelkwatar daga hannunsu a shafukansu na sada zumunta.
Read Also:
Amma Shafin intanet da ke goyon bayan dakarun RSF ya rawaito cewa babban jami’in RSF ya sha alwashin “mai da martani mai zafi” yayin da ya ce har yanzu babban birnin Khartoum na hannun mayaƙansu.
Yaƙin da aka kai watanni sha ɗaya ana gwabzawa kan kwatar ikon babban birnin na ci gaba duk da kiran da majalisar dinkin duniya tayi kan samar da yarjejeniyar da za ta bari a shigar da kayan agaji da ake bukata cikin Sudan yayin azumin watan Ramadan.
Ƙwace shelkwatar gidan labaran gagarumar nasara ce ga sojojin abin da ya dade yana ci wa sojojin tuwo a ƙwarya.
Wannan na nufin cewa kusan duka birnin Omdurman ya koma ƙarkashin ikon sojojin kuma hakan alama ce ta ƙokarinsu na sake mayar da babban birnin karkashin ikon gwamnati daga hannun RSF.