Kotu ta Sanar da Ranar da za ta Ci gaba da Sauraren Karar Miki Abba Kyari Amurka
A yau ne wata babbar kotun tarayya ta bayyana ranar da za ta ci gaba da sauraran shari’ar mika Abba Kyari kasar Amurka.
Ana zargin Abba Kyari ne da hannu a wata damfara da fitaccen dan damfarar yanar gizo; Hushpuppi ya yi a Qatar.
Ana ta kai ruwa rana tun bayan da wata kotu a Amurka ta nemi gurfanar da dan sandan kan alakarsa da Hushpuppi.
Read Also:
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sa ranar Juma’a za ta ci gaba da sauraren karar mika ACP Abba Kyari da aka dakatar zuwa hannun Amurka, The Nation ta rawaito.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya zabi ranar ne a ranar Alhamis domin baiwa babban lauyan gwamnati damar shigar da kara a hukumance a kan batun da Kyari ya shigar na kin amincewa da matakin farko na kalubalantar cancantar mika shi da AGF ya shigar.
AGF ya nemi kotu ta ba ta izinin mika Kyari ga hukumomin Amurka dangane da alakarsa da wanda ake zargi da damfara ta yanar gizo, Abbas Ramon (wanda aka fi sani da Hushpuppi).
Karin bayani na nan tafe..