Yancin Kai: Gwamnatin Tarayya ta Ayyana Ranar Litinin, 2 ga Watan Oktoba a Matsayin Ranar Hutu
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin hutun ranar ‘yancin kai.
Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis.
Ministan ya kuma taya yan Najeriya na gida da waje murnar bikin ranar ‘yanci.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu don bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun yancin kai.
Olubunmi Tunji-Ojo, wata sanarwa da ministan harkokin cikin gida ya yi a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba a madadin gwamnatin tarayya, ya ayyana Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu, rahoton The Nation.
Ministan Tinubu ya taya ‘yan Najeriya murnar samun ‘yancin kai
Read Also:
A cikin sanarwar tasa, ministan ya taya ‘yan Najeriya na gida da waje murnar samun ‘yancin kai.
A cikin sanarwar da ke dauke da sa hannun sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Oluwatoyin Akinlade, ministan ya bayyana jajaircewar gwamnatin tarayya na tunkarar kalubalen da ke addabar kasar.
Sanarwar ta ce:
“Sanannen abu ne a yau cewa matsalolin tattalin arziki da tsaro abu ne da suka addabi duniya, kuma ba a ware Najeriya ba.”
Ministan harkokin cikin gida ya yi magana kan kokarin gwamnati
Ya kara da cewar gwamnati na kokari don dakile tarin kalubalen da ke tunkarar kasar kuma za ta ci gaba da yin hakan har sai an samu sauki a kasar, rahoton Daily Trust.
Tunji-Ojo ya jaddada cewa babban matsayin Najeriya a kasashen duniya da ci gaban da ke tunkaro kasar abu ne da za a iya cimmawa idan muka yi aiki tare cikin hadin kai.
A cewar ministan, Najeriya za ta ci gaba da zama abin alfaharin Afirka, kuma za ta kasance wani ginshiki ga ajandar Shugaba Bola Tinubu.