Kotu ta Ayyana Zaben Gwamnan Kaduna a Matsayin Wanda Bai Kammala ba

 

Kotun zaben gwamnan jihar Kaduna ta soke nasarar zaben Gwamna Uba Sani.

Da take yanke hukunci a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, kotun ta ayyana zaben gwamnan jihar Kaduna a matsayin wanda bai kammala ba.

Sakamakon wannan hukunci da ta yanke, ta umurci hukumar INEC da ta sake sabon zabe a jihar cikin kwanaki 90.

Jihar Kaduna – Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zama a jihar Kaduna, ta soke nasarar Gwamna Uba Sani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

Kotu ta ayyana zaben gwamnan Kaduna a matsayin wanda bai kammala ba

Kotun ta kuma ayyana zaben gwamnan na jihar Kaduna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba wato ‘inconclusive’.

Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, kotun ta bayar da sanarwar ne yayin da take yanke hukunci ta manhajar Zoom kan shari’ar zaben a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Isah Ashiru ne suka shigar da kara kotu suna masu kalubalantar zaben Uba Sani.

Kotun zaben ta yi umurnin cewa a gudanar da sabon zabe a gudunmomi bakwai a kananan hukumomi hudu na jihar, rahoton Daily Post.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com