Karamar Hukumar Rano ta Jahar Kano ya Hana Zancen Dare

 

An saka dokar hana yin zancen dare tsakanin samari da ‘yan mata a karamar hukumar Rano ta jahar Kano.

Tuni dai an umurci ‘yan Hisbah da sauran jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana saba sabuwar dokar.

Shugaban karamar hukumar tare da mahukunta sun saka dokar ne don dakile badalar da ake aikatawa tsakanin mata da maza yayin zancen dare.

Rano, Jahar Kano – Karamar hukumar Rano a Jahar Kano, a ranar Laraba ta amince da kafa dokar hana tadi ko haduwa tsakanin samari da ‘yan mata da dare a jahar, Premium Times ta rawaito.

Karamar hukumar ta ce an saka wannan dokar ne saboda samun yaduwar badala da ake aikatawa tsakanin samari da yan mata har ma da zaurawa a yankin.

A cewar rahoton na Premium Times, karamar hukumar ta ce daga yanzu masoya suna iya haduwa ne kawai da rana domin yin tadi.

A cewar jami’in watsa labarai na karamar hukumar, Habibu Faragai, shugaban karamar hukumar, Dahiru Muhammad, ya sanar da dokar ne yayin taron tsaro da masu sarautun gargajiya da mazauna garin suka hallarta.

Mr Muhammad ya ce kwamitin ta tattauna game da karuwar ayyukan badala a karamar hukumar, ya kara da cewa hakan ne yayi sanadin kafa sabuwar dokar.

Dalilin saka dakar hana zancen daren?

Ya ce an kafa dokar ne domin tsaftace karamar hukumar daga ayyukan badala da ake aikatawa cikin dare tsakanin maza da mata.

Shugaban karamar hukumar ya umurci Hukumar Hisbah da sauran hukumomin tsaro a karamar hukumar su tabbatar ana bin dokar tare da kama wadanda suka saba.

Kazalika, Hakimin Rano, Mannir Tafida-Abubakar, ya yi kira ga mazauna kauyen da dagatai da masu unguwanni da limamai su tabbatar mutane suna bin dokar.

Mr Tafida-Abubakar ya ce akwai kimanin manyan abubuwa uku masu alaka da tabarbarewar tarbiyya da ke ciwa mutanen garin tuwo a kwarya.

Basaraken ya ce:

“Mafi yawancin iyaye sun yi na’am da dokar kuma suna goyon baya. Idan iyaye ba su bada hadin kai ba, kuma wadannan abubuwan suka sake faruwa, kowa zai ga sakamakon sakacin.”

Gwamnatin Jahar ta hana mata da maza hawa adaidaita sahu na haya guda daya tun shekarar 2019.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here