An Rantsar Janar Tchiani a Matsayin Shugaban Riƙo na Jamhuriyar Nijar
An rantsar da Janar Abdouramane Tchiani a matsayin shugaban riƙo na Jamhuriyar Nijar, wanda zai kwashe shekara biyar yana jan ragamar gwamnati kafin miƙa mulki.
Hakan wani ɓangare ne na aiwatar da rahoton babban taron ƙasar da aka yi a watan Fabairun da ya gabata.
Read Also:
A lokacin shan rantsuwar a ranar Laraba, Tchiani ya kuma zama janar ɗin soja mai tauraro biyar, wanda hakan na daga cikin shawarar taron ƙasar.
Bikin rantsarwar da aka yi a babban ɗakin taro da ke birnin Yamai ya samu halartar sojoji da kuma manyan masu ruwa da tsaki a ƙasar.
Kafin shan rantsuwar na yau, janar Tchiani ya kasance shugaban majalisar ceton ƙasa, wadda aka kafa tun bayan kifar da gwamnatin Muhammed Bazoum.