Alaƙa da ‘Yan bindiga: Sababbin Kwamishinonin Zamfara Sun Rantse da Kur’ani
Gwamnan jahar Zamfara Bello Matawalle ya rantsar da sabbin kwamishinoni da sakatarorin gwamnati da masu ba shi shawara a yau litinin.
Kwamishinonin sun rantse da Allah da kuma Al Kur’ani mai tsarki cewa ba su da hannu ko alaƙa da ƴan bindiga da suka addabi jahar.
Rantsuwar da kwamishinonin suka yi rungume da Al-Kur’ani ta ƙunshi cewa:
“Billahillazi La’ilaha illahuwa, na rantse da Allah cewa ban taɓa shiga sha’anin ta’addanci ba, a jahar Zamfara ko kuma na yi amfani da wata dama da Allah ya ba ni domin in nuna jin dajin ana kashe al’umma ko salwantar da dukiyarsu. Haka kuma ban taɓa jin daɗin aikin ta’addanci da ke gudana a cikin jahar nan ko kuma a wajenta ba.
“Idan ina da hannu a cikin ta’addancin kar Allah ya ba ni lamuni ko da na dakika ɗaya. Haka kuma ba zan yi amfani da mukamina ba domin taimakawa wajen aikin ta’addanci ko salwantar da dukiyar jama’a. Idan na yi haka kar Allah ya ba ni abin da nake nema duniya da lahira.”
Jahar Zamfara na cikin jahohi a arewacin Najeriya da suka fi fama da matsalar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa da kuma hare-haren ‘yan fashin daji.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here