‘Yan IPOB ba su Kai ‘Yan Bindigan Arewa Gurbacewa ba – Gwamna Okezie Ikpeazu
Okezie Ikpeazu, gwamnan jahar Abia ya tabbatar da cewa a shirye ya ke da ya tattauna da ‘yan awaren IPOB.
 A cewar gwamnan jahar Nnamdi Kanu, ‘yan awaren IPOB ba su kai ‘yan fashin dajin arewacin Najeriya gurbata ba.
 Gwamnan ya ce har yau dan kasa ya ke kallon Nnamdi Kanu kuma ya fi masu kwashe malamai da dalibai daga makarantu.
Abia – Okezie Ikpeazu, gwamnan jahar Abia, ya ce ‘yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB) ba su kai ‘yan bindigan arewa gurbacewa ba.
A yayin tattaunawa da jaridar Vanguard, gwamnan ya ce hanyar da ta fi dacewa a shawo kan matsalar masu tada kayar bayan shi ne gwamnatin tarayya ta tatauna da su.
Ya ce akwai sakon da IPOB ke kokarin aikawa kuma akwai bukatar kowa ya tsaya tsayin daka.
“Dole ne mu tattauna da IPOB. Eh, dole ne mu samu hanyar tattaunawa da su. Wadannan mutanen ba su kai wadanda ke arewa maso gabas ko arewa maso yamma fitina ba.
 Masu zuwa makarantu kuma su kwashe malamai da dalibai ko kuma su shiga masallaci ko coci su kwashe masu bauta,” yace.
“Na yadda cewa akwai wani abu da mutanen nan na yankin kudu maso gabas ke bukata. Akwai wani abu da ya dace a saurara daga wurinsu duk da laifi da ta’addanci ne su dauka makamai.
“Akwai sakon da su ke kokarin aikewa a hakan. Dole ne mu kasance masu karfin guiwa a maimakon amfani da kalaman da basu dace ba a matsayinmu na shugabanni. Najeriya zaune ta ke a kan bam amma kuma hanyar shawo kan matsalar ba ta da wuya.”
Gwamnan Abia ya ce a matsayinsa na gwamnan jahar da Nnamdi Kanu ya fito daga, ya dauke shi a matsayin dan kasa ba wai shugaban kungiyar IPOB ba inda ya kara da cewa ya shirya sasanci da ‘yan kungiyar domin samun maslaha, TheCable ta wallafa.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here