Rarara: Wata Kotun Kano ta Bukaci da Mawakin ya Gurfana a Gabanta
Babbar kotun shari’a da ke Kano ta bukaci Dauda Kahutu Rarara ya bayyana a gabanta kafin ranar 22 ga watan Disamba.
Hakan ya biyo bayan korafin da mijin wata mata ya kai gaban kotu bayan Rarara ya tsere masa da matarsa.
A cewar mijin, watanni 3 kenan da ya nemi matarsa ya rasa tun bayan ta bayyana a wani bidiyon wakar Rarara.
Read Also:
Babbar kotun shari’a ta Kofar Kudu da ke jihar Kano ta gayyaci babban mawakin Shugaba Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara, inda ta bukaci ya gabatar da kansa gaban kotu kafin ranar 22 ga watan Disamba a kan zargin boye wata matar aure, wacce yayi wani bidiyon wakarsa.
Bayan mijin matar ya gabatar da korafinsa a gaban kotun, inda ya zargi mawakin da amfani da matarsa, matar aure a bidiyon wata wakarsa mai taken ‘Jihata’, wanda tun bayan nan bai sake ganinta ba.
Ya kai korafin gaban kotu bayan ya yi watanni 3 cur, ba tare da ya san inda matarsa take ba, kuma ya bukaci kotun da tayi masa adalci a kan wannan wulakanci da aka yi masa, Daily Trust ta tabbatar.
Alkalin kotun musuluncin, Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya dage sauraron shari’ar zuwa 22 ga watan Disamba don Rarara ya bayyana a gaban kotu, a cigaba da sauraron shari’ar.