Fatima Yarinya Wadda Ke Rarrafe Cikin Tsakiyar Rana Domin Zuwa Makaranta

 

Tare da cewar rana mai zafi na tsananin dukanta,harma ta ratsa fatar ta,ta keta ta shiga cikin jinin jikinta,amma marainiya Fatima haka take tsantsar kaunar zuwa makaranta.

Binciken Arewa Agenda yayi nuni ga yadda Fatima,wadda ke da nakasa ta kafa da hannu dake aji biyu a firamaren Makarantar Danshayi a karamar hukumar Rimin Gado ke jure dukkan wahala tayi rarrafe mai tsaho sama da kilomita daya har zuwa makaranta,zuwa da kuma dawowa kullum.

“Tana matukar son karatu da zuwa makaranta,batason fashi ko kadan.”Inji malamin ta na makaranta.

Lokacin da tawagar Jaridar Arewa Agenda suka kai ziyara gidan su Fatima bisa jagorancin Hedimastan makarantar su,Ahmadu Ali,sun riski fuskarta cikin matukar walwala sabili da tozali da fuskar hedimastan ta,murmushin daya kasa gushewa har tsawon lokaci.

Fatima bata iya tafiya kwata kwata,hakika tana bukatar Wilciya( Wheelchair) dazai taimaka mata wajen cimma muradin ta na yin karatu.

A yayin zantawa da Jaridar Arewa Agenda, kakar Fatima tace haihuwar Fatima da kwanaki kadan suka kwanta rashin lafiya ita da mahaifiyar ta,maihaifin Fatima ya saki mahaifiyar ta wata biyar bayan haihuwar ta,a cewar sa bazai iya daukar nauyi jigilar samun lafiyar su ba.

Yayin tuntubar ko anyiwa Fatima allurar Riga Kafi ko akasin haka,take anan kakar ta nunawa Arewa Agenda alamar inda aka yimata.

Mahaifiyar Fatima ta mutu wata takwas baya,yanzu haka Fatima na zaune a garin Karofin Yashi,a kauyen Danshayi.

Tare da ok karatu na Fatima,watakil ba lallai ta samu ingantacce ba,saboda makarantar Danshayi na tattare da tarin matsaloli.

Silin din makarantar ya lalace matuka,kofofi da winduna sun lalace gaya ,gashi babu teburin zama,babu kyakkyawan yanayi karatu kwata kwata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here