Mutane 7 Sun Rasa Rayukansu a Harin da ‘Yan Bindiga Suka Kai Filato

 

Akalla mutum bakwai ne aka kashe a wani harin da yan bindiga suka kai a karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar Filato a tsakiyar Najeriya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Harin na zuwa kasa da awa 24 bayan kashe wasu mutum 18, a taho mu gama tsakanin mahara da kuma ‘yan banga a karamar hukumar Wase da ke jihar.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa harin ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe tara na dare.

Ta ambato mai magana da yawun kungiyar matasan Birom Rwang Tengwong, yana cewa ”yan bindiga sun kashe mutum bakwai a kauyen Danda Chugwi, kuma wasu sun jikkata da yanzu haka ke jinya a asibitin Vom.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here