Mutane 11 Sun Rasa Rayukansu a Harin da ‘Yan Bindiga Suka Kai ƙaramar Hukumar Safana Dake Jahar Katsina

 

Wasu yan bindiga sun kai hari a garin Tsatskiya dake ƙaramar hukumar Safana, jahar Katsina inda suka hallaka mutum 11 tare da jikkata wasu da dama.

Maharan sun isa garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Ranar Asabar domin ɗaukar fansa a kan kisan da mutanen garin suka yi wa ɗan leƙen asirinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa kwana huɗu kafin harin mazauna garin sun gano wani ɗan leƙen asiri dake aiki da yan bindiga kuma suka kashe shi.

Aƙalla mutane 11 wasu yan bindiga suka hallaka yayin da mutum uku suka samu raunuka a garin Tsatskiya dake ƙaramar hukumar Safana, jahar Katsina.

An garzaya da Mutane uku da suka sami raunuka asibitin Dutsin-ma domin samun kulawa ta musamman. Rahoton Dailytrust ya bayyana cewa maharan sun farmaki garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar ranar Asabar.

Ana zargin dai maharan sun kawo harin ne domin ɗaukar fansa bisa kisan da mazauna garin suka yiwa ɗan leƙen asirin su. Kwanaki huɗu kafin kawo harin, mutanen garin sun gano wani ɗan leƙen asiri dake aiki da yan bindiga suka kashe shi.

Wata majiya ta bayyana cewa yan bindigar sun isa garin ne a kan mashina, inda suka buɗe wuta kan me uwa da wabi wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 11.

Mutanen garin Tsatskiya sun kwarara zuwa Dutsin-ma domin tseratar da rayuwarsu. Kakakin hukumar yan sandan jahar Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya musanta adadin da ake yaɗawa cewa mutum 11 ne suka rasa rayukansu.

Yace: “Mun samu rahoton kai hari ƙauyen Tsatskiya kuma mutane uku ne suka rasa rayukansu ba 11 ba kamar yadda ake yaɗawa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here